26 Disamba 2019 - 06:42
Sarkin Musulmi Yayi Watsi Da Ikirarin CAN Na Nuna Wariyar Addini A Najeriya

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III yayi watsi da ikirarin kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN na cewa ana musgunawa Kiristoci a Nijeriyan, biyo bayan wani rahoto da Amurka ta fitar inda ta zargi gwamnatin Najeriyar da take hakkin ‘yan kasar na ‘yancin addini.

(ABNA24.com) Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III yayi watsi da ikirarin kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN na cewa ana musgunawa Kiristoci a Nijeriyan, biyo bayan wani rahoto da Amurka ta fitar inda ta zargi gwamnatin Najeriyar da take hakkin ‘yan kasar na ‘yancin addini.

Sultan Sa’ad Abubakar ya ce idan ma har akwai irin wannan abin da kungiyar ta CAN take ikirari, to da kuwa an tattauna kan hakan a majalisar tattaunawa ta addinai inda musulmi da kiristoci suke taruwa don tattauna batutuwan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Sarkin musulmin ya kara da cewa: mafi yawa daga cikin ayyukan ta’addancin da ake zargin Fulani makiyaya suna aikatawa, suna aikata hakan ne ba wai saboda addini ba, don kuwa ba dukkanin Fulani din ne musulmi ba. Don haka sai ya ce wannan ikirari na CAN din magana ce kawai maras tushe.

A kwanakin baya ne dai Amurka ta fitar da wani rahoto inda tace ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da za ta sanya ido kansu saboda zargin take hakkokin ‘yan kasar na zaban addinin da suke so, lamarin da kungiyar CAN din ta goyi baya amma gwamnatin kasar ta musanta.



/129