21 Disamba 2019 - 08:14
​Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince da Tsige Trump

Majalisar wakilan Amurka mai rinjayen 'yan jam'iyyar demokirat, ta kada kuri'ar tsige shugaba Domald Trump, bisa zarginsa da amfani da ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba da hana majalisa yin aikinta.

(ABNA24.com) Majalisar wakilan Amurka mai rinjayen 'yan jam'iyyar demokirat, ta kada kuri'ar tsige shugaba Domald Trump, bisa zarginsa da amfani da ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba da hana majalisa yin aikinta.

'Yan majalisar wakilai 230 ne suka goyi bayan tsige shugaban yayin da 197 suka ki amincewa.

Laifukan Mista Trump sun hada da kokarin tilasta wa shugaban Ukraine da ya binciki abokin hamayyarsa, a zabe mai zuwa, cewa da tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden, da kuma kokarin kawo wa majalisa tarnaki.

Trump a yanzu ya zamo shugaban Amurka na uku da ya taba fuskantar irin wannan tsigewa daga majalisar wakilai.

Yanzu dai batun zai koma ga majalisar dattawa da yan jam'iyyar Republican da Trump ke da rinjaye wacce zatayi zama a cikin watan Janairu na shekara mai shirin kamawa domin yi masa shari'a.


/129