11 Disamba 2019 - 05:57
 Zarif : Iran A Shirye Take Tayi Musayar Fursunoni Da Amurka

Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa Tehran a shirye take ta yi musayar fursunoni da kasar Amurka don haka Zabi ya ragewa kasar ta Amurka.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa Tehran a shirye take ta yi musayar fursunoni da kasar Amurka don haka Zabi ya ragewa kasar ta Amurka.

Cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na Twitter a jiya Litinin Ministan harakokin wajen kasar ta Iran ya yi ishara kan dowowar wasu fursunonin kasar Iran da Amurka gida, inda ya kara da cewa a halin da ake ciki mahukuntan Tehran a shirye suke da yi musayar fursunoni da kasar Amurka don haka Zabi ya ragewa kasar Amurka.

A daren Asabar din da ta gabata ce Dr. Soleimani ya iso filin jirgin saman Mehrabad da ke birnin Tehran tare da ministan harkokin wajen Iran din Dr. Muhammad Jawad Zarif, bayan an sako shi daga Amurka sakamakon wani musayen fursunoni da aka cimma tsakanin Iran da Amurka a birnin Zurich na kasar Switzerland.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai jim kadan bayan isowarsa birnin Tehrain , Dr. Soleimani ya ce irin nasarorin da Iran take samu a fagen ilimin kimiyya da fasaha na daga cikin abubuwan da suke sanya Amurka fushi da kuma gaba da Iran din, yana mai kiran masanan Iran da su ci gaba da kokarin da suke yi wajen ciyar da kasar gaba kamar yadda kuma ya gode wa jami’an Iran saboda kokarin da suka yi wajen sanya a sako shi daga Amurkan.


/129