11 Nuwamba 2019 - 05:33
​Taron Hana Yaduwar Makaman Nukiliya A Moscow

An fara gudanar da taron kasa da kasa kan hana yaduwar makaman nukiliya yankin gabas ta tsakiya a birnin Moscow na kasar Rasha.

(ABNA24.com) An fara gudanar da taron kasa da kasa kan hana yaduwar makaman nukiliya yankin gabas ta tsakiya a birnin Moscow na kasar Rasha.

Tashar pressTV ta bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da zaman taron ne tare da halartar wakilai daga kasashen duniya daban-daban, inda mataimakin ministan harkokin harkokin wajen kasar ta Rasha Sergey Riyabkov ne ya bude taron da jawabinsa.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa, Riyabkov ya bayyana cewa, daya daga cikin abubuwan da suke da matukar muhimamnci a halin yanzu shi ne tabbatar da cewa an kare yarjejeniyar nukiliya ta duniya da aka rattaba hannuakanta tare da Iran.

Ya ce akwai yiwuwar wannan yarjejeniya ta rushe, bayan da kasashen yammacin turai suka nuna gazawa a gaban kasar Iran ta hanyar kasa cika alkwullan da suka dauka mata, bayan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar.

Riyabkov ya ce dole ne kasashen Amurka da kuma kasashen turai su fahimci irin gagarumin hadarin da yake tattare da rushewar wannan yarjejeniya, da kuma abin da ka iya biyo bayan hakan.



/129