23 Oktoba 2019 - 10:48
Za’ayi Taro Kan Rikicin Afganistan A Birnin Pekin

Kungiyar Taliban ta sanar da cewa za’a gudanar da wani taro na tsakanin ‘yan Afganistan a brining Pekin na kasar China, domin lalaubo hanyoyin matsalolin da kasar ta Afganistan ke fama dasu.

(ABNA24.com) Kakakin kungiyar Taliban ne, Suhail Shaheen, ya sanar da hakan ga kamfanin dilancin labaren AFP, saidai bai fayyace ko wadanne bangarori zasu halarci taron ba.

Amma a cewarsa tawagar kungiyar zata isa a birnin na Pekin a ranakun 19 da 30 ga watan Oktoba nan.

An dai cimma wannan matsaya ce bayan wata ganawa a Doha, tsakanin shugaban ofishin siyasa na kungiyar ta Talibanda kuma wakilin musamman na kasar China, Deng Xijon.

Saidai kawo yanzu babu wani bayyani daga gwamnatin ta Afganistan kan taron.

........
340