(ABNA24.com) Babban malamin addini na kasar Bahrain Sheikh Isa Kasim ne ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; tabbas gaskiya za ta kai ga yin nasara idan har aka sami hadin kai a tsakanin bangarori daban-daban na al’umma.
Sheikh Isa Kasim ya kara da cewa; Gwagwarmaya wani nauyi ne wanda ya rataya a wuyan kowa da kowa ba akan wasu tsiraru a cikin al’umma ba.
Tun a ranar 9 ga watan Yuli na 2018 ne dai aka Shehin malamin na kasar Bahrain zuwa kasar Ingila domin yin jiyyar rashin lafiyar da yake fama da ita.
Tun a 2011 ne dai al’ummar Bahrain su ka bi sahun ‘yan’uwansu larabawa wajen neman ‘yanci daga tsarin kama-karya na sarakunan larabawa
Da dama daga cikin jagororin yunkurin na al’ummar Bahrain an kame su, tare da yanke musu hukunci mai tsauri a gidajen kurkuku.
A jiya Laraba ma dai jami’an tsaron kasar ta Bahrain sun kama Sheikh Sa’id al-Usfur, wanda daya ne daga cikin masu rajin kawo sauyi a cikin kasar.
ظ129
28 Satumba 2019 - 04:45
Lambar labari: 978565
Babban malamin addini na kasar Bahrain Sheikh Isa Kasim ne ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; tabbas gaskiya za ta kai ga yin nasara idan har aka sami hadin kai a tsakanin bangarori daban-daban na al’umma.