26 Satumba 2019 - 04:23
Salami:Yardar Da Karfin Da Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Ta Samu Zai Yi Wa Makiya Wahalar Yarda Da Ita

Yayin da yake ishara kan gwagwarmayar al'ummar kasar Yemen, Babban kwamandar Dakarun juyin juya halin musulinci ya ce karfin da kungiyar Ansarullah ta samu a yau, da wahala makiya su yarda da ita.

(ABNA24.com) Yayin da yake ishara kan gwagwarmayar al'ummar kasar Yemen, Babban kwamandar Dakarun juyin juya halin musulinci ya ce karfin da kungiyar Ansarullah ta samu a yau, da wahala makiya su yarda da ita.

Manjo-janar Husein Salami ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a daren jiya Talata a nan birnin Tehran, babban kwamandan Dakarun juyin juya halin musulinci ya ce yana da wuya makiya su amince da irin karfin da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen take da shi a yau, domin a baya dakarun tsaron kasar yemen ba su da karfin kare kasarsu, an kwashe sama da shekaru 4 ana kawo musu hari, a kashe mutanansu a rusa dukkanin wasu wurare masu mahimanci na kasar, amma a yau kasar ta kai matsayin da za ta kai hare-hare kan kasashen da suke kawo mata hari, wannan ba abu ba ne mai sauki ga makiya su amince da wannan karfin na kungiyar Ansarullah.

Yayin da yake ishara kan zarkin da makiya ke yiwa jamhoriyar musulinci ta Iran na cewa tana da hanu a harin da aka kai kan cibiyoyin man fetir din kasar Saudiya, Manjo Janar Salami ya ce Yamaniya suka kai harin ramuwar gayya kan irin gisan killar da ake yi wa al'ummarsu, amma makiya na alakanta hakan da jamhoriyar musulinci ta Iran.



/129