(ABNA24.com) Mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Al-shabab sun kai farmaki kan wani barikin soja a kusa da birnin Magadushu na kasar Somaliya tare da kwashe makamai masu yawa.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya ruwaito majiyar tsaron kasar Somaliya na cewa da misalin karfe 5:30 na safiyar yau Lahadi, mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Al-shabab sun afkawa wani barikin soja mai nisan kilomita 60 da birnin Magadushu fadar milkin kasar, da farko dai maharan sun kai harin kunar bakin wake da mota shake da bama-bamai, kafin daga bisani su kutsa cikin barikin suka kashe sojojin da kwashe makaman yaki masu yawa.
Wani Dattijon yankin mai suna Ahmad Kaali ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuteus cewa sun wayi gari da karar tashin bama-bamai, da musayar wuta tsakanin 'yan bindigar da sojoji, sannan kuma an ga 'yan bindigar suna ficewa daga barikin Sojan daukan da motoci shake da makaman yaki.
Wani Soja da ya bukaci a sakaye sunansa ya ce harin ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkata Sojoji da dama.
Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta Al-shabab mai alaka kut da kut da kungiyar AlQa'ida ta dauki alhakin kai harin, cikin wata sanarwa da mai magana da sunan kungiyar Abdul-Aziz Abu Mus'ab ya fitar ya ce mujahidai sun kashe Sojoji 23 sannan kuma sun samu nasarar kwato makaman yaki masu yawa da suka hada da manyan makamai masu kakkabo jiragen yaki.
/129
23 Satumba 2019 - 04:30
Lambar labari: 977333
Mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Al-shabab sun kai farmaki kan wani barikin soja a kusa da birnin Magadushu na kasar Somaliya tare da kwashe makamai masu yawa.