24 Agusta 2019 - 08:24
Dakarun Sojin Kasar Siriya Sun Karbe Ikon Kula Da Garin Khan Shaikhun A Idlib

Rahotanni da suka fito daga kasar Siriya sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Siriya sun karbe ikon garin shaikhun dake gefekudancin garin Idlib,kum suna ci gaba da kwance nakiyoyi da bama bama..

(ABNA24.com) Rahotanni da suka fito daga kasar Siriya sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Siriya sun karbe ikon garin shaikhun dake gefekudancin garin Idlib,kum suna ci gaba da kwance nakiyoyi da bama bama da aka dasa a kan hanya , wanna yana nufin yankunan kufr zina da damina da muruk da ladma dake gefen arewan hama duk sun koma karkashin ikon sojojin na Siriya

Majiyar ta ci gaba da cewa karbe iko da garin da sojoji suka yi zai bude musu hanya wajen ci gaba da samun gagarumar nasarana na karbe sauran yankunan daga hannun yan ta’adda da suka hada da arewacin garin garin ma’arat Nuaman inda hanyoyi suka hade da hanyoyin da kasar ta yi iyaka da hanyoyin kasa da kasa ta gabas ta yamma da arewa da kudanci.

A gefe guda kuma dakarun kasar Siriya sun bude wata kofa domin bada dama ga fararen hula su fice daga yankin arewa masu gabashin garin Idlib da wadanda ke makwabtaka da Hama domin tsirawa daga yakin da akeyi.


/129