Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Babban Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Iran Janar Mohsen Rezaei, a daren Asabar a shafin X ya rubuta cewa: Mun sha faɗa cewa dole ne a cika sharuɗɗa bakwai da Iran ta sanar. Idan an cika sharuɗɗan, hanyar diflomasiyya a buɗe take.
Ya kara da cewa: A sabanin haka kuwa idan aka ɗauki wani mataki a kan ƙasar, bisa ga umarnin da Babban Jagora ya ba sojoji a yau, za mu kai wa masu zalunci mummunan hari da sabbin makamai.
…………
Ra'ayinka