6 Agusta 2019 - 07:10
Cana Ta Dakatar Da Sayan Kayakin Noma Daga Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cana ta bada sanarwan a safiyar yau talata kan cewa kasar ta dakatar da sayan kayakin noma daga kasar Amurka saboda takunkuman da Amurka ta yi barzanar zata dorawa kasar a cikin watan satumba mai zuwa.

(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cana ta bada sanarwan a safiyar yau talata kan cewa kasar ta dakatar da sayan kayakin noma daga kasar Amurka saboda takunkuman da Amurka ta yi barzanar zata dorawa kasar a cikin watan satumba mai zuwa.

Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta bayyana cewa, ma’aikatar ba ta bayyan kimar kayakin noma da ta dakatar da sayansu daga kasar Amurka ba, amma ta kara da cewa zata dora haraji kan kayakin noma da aka yi cinikinsu kafin ranar 3 ga watan Augustan da muke ciki a Amurkan.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya bada sanarwan cewa gwamnatinsa zata kara kakabawa kayakin Cana haraji na kasha 10% wanda zai kai dalar Amurka biliyon 300 daga watan satumba mai zuwa, saboda ta ki sayan kayakin noma daga kasar ta Amurka.

Wannan matakin da kasar Cana ta dauka a yau dai ya kara dagula harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, sannan tabbas wannan matakin zai shafi sauran cibiyoyin kasuwanci a duniya.



/129