(ABNA24.com) Kafar watsa labaru ta Nyasa Times wacce ta buga labarin ta ci gaba da cewa; Gwamnatin kasar ta Malawi da kuma kungiyoyin fararen hula suna bayyana damuwarsu akan yadda ake kara samun karuwar mutanen kasar da suke kawo karshen rayuwarsu da kansu
Wata kididdiga da jami’an ‘yan sandan kasar ta Malawi ta fitar, ta bayyana cewa; Daga watan Satumba na 201 zuwa watan Yuni na wannan shekara ta 2019, an sami mutane 133 da su ka kashe kawukansu. Kididdigar ta ci gaba da cewa; mutanen da su ka kashe kawukansu, shekarunsu suna kamawa ne daga 16 zuwa 40.
Babban darakta a cibiyar bunkasa rauywar matasa, Lucky Mbewe ya bayyana cewa; Gwamnati ce take da laifi, saboda gajiyawarta wajen samarwa da samarin kasar damar da za su gina rayuwarsu.
/129
30 Yuli 2019 - 06:22
Lambar labari: 965748
Kafar watsa labaru ta Nyasa Times wacce ta buga labarin ta ci gaba da cewa; Gwamnatin kasar ta Malawi da kuma kungiyoyin fararen hula suna bayyana damuwarsu akan yadda ake kara samun karuwar mutanen kasar da suke kawo karshen rayuwarsu da kansu