25 Yuli 2019 - 07:09
​​An Isar Da Sakon Shugaba Ruhani Ga Shugaban Kasar Faransa

Dan sakon shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani zuwa ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isar da sakon a jiya Talata.

(ABNA24.com) Dan sakon shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani zuwa ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isar da sakon a jiya Talata.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya bayyana cewa wasikar shugaba ruhadi tana dauke da sakonni wadanda suka hada da dangantakar kasashen biyu, mastalolin yankin gabas ta tsakiya, da kuma ta yadda kasashen turai zasu wanzarda yerjejeniyar nukliyar kasar iran ta shekara ta 2015.

Kafin ganawarsa da shugaban kasar na faransa Abbas Arachi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Faransa inda a nan ma suka tattauna lamura da suka shafi matsalolin yankin gabas ta tsakiya da kuma hanyoyin warwaresu.

Kasashen faransa, jamus da Britania suna daga cikin kasashen Turai da suka sanya hannu a kan yerjejeniyar nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015.


/129