Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya habarta cewa alkalai dake bincike kan cin hanci da rashawa da barnar dukiyar kasa sun fara binciken hambararen shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
A ranar alhamis din da ta gabata ce alkalin alkalan kasar Sudan din ya bayar da umarnin fara gudanar da binciken hambararen shugaban kasar Omar al-bashir kan zargin da ake yi masa na halasta kudaden haram da kuma taimakon kudi da yake bawa 'yan ta'adda.
Gurfanar da manyan jami'an gwamnatin hambararen shugaban kasar Sudan da makusantansa a gaban kuliya na daga cikin bukatun 'yan kasar Sudan da suka yi bori ga majalisar Sojin kasar tun bayan da suka riki madafun ikon kasar ta Sudan.
A watan Afirilun da ya gabata ne babban alkalin kasar Sudan din ya gano cewa hambararen shugaban kasar nada alaka da masu halasta kudaden haram bayan wani bincike da aka yi, lamarin da ya sanya aka binciki gidansa inda aka gano wasu milyoyin dalar Amurka a cikin gidan nasa.