Majiyar MDD ta ce; Za a yi taron ne dai domin karfafa rawar da diplomasiyya da kuma aiki tare suke takawa wajen samar da zaman lafiya, wanda za a bude a gobe Laraba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; Taron na wuni daya ya kunshi gabatar da jawabai daga maharta taron, acikin mintuna uku.
A shekarar 2018 da ta gabata ce Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya shelanta ranar 24 ga watan Aprilu a matsayin ranar diplomasiyya da kuma aiki tare a tsakanin al’ummu, domin tabbatar da zaman lafiya.