Shugaba Buhari ya ce rashin adalci ne a ce gwamnatinsa ta kauda ido a kan kisan kiyashin da ake yi wa al’umma a jihar ta Zamfara, domin an aike da jami’an tasaro zuwa lungu da sako inda abin ke faruwa kuma muna kara azama.
Shugaban ya kara da cewa kare dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya su ne abin da na saka a gaba a kodayaushe. Babu wani abu da ya sha gaban haka.sannan ya ce a kodayaushe ina samun bayanai daga jami'an tsaro a kan abin da ke faruwa a kasa baki daya. Ina tabbatar maku cewa za mu ci gaba da yin iyakar kokarinmu don karfafa wa jam'ian tsaro gwiwa su tunkari lamarin da karfin da ya dace.
Har ila yau Shugaba Buhari ya bukaci da 'yan Najeriya da kada su siyasantar da wannan al'amari na Zamfara, sa’anan ya yi amfani da wannan dama ne mika sakon ta'aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa da kuma 'yan uwansu da masoyansu. Inda ya ce Muna jin abin da kuke ji kuma babu abin da ya fi muhimmanci a wurina sama da in ga an kawo karshen wadannan 'yan fashi.