Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran, ya nakalto Zareef yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake hira da jaridar "Hamshahri na kasar ta Iran.
Ministan ya kara da cewa Iran ta sha tattaunawa da kasar Britania dangane wadannan kudade, sannan ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa ta Hague wacce ta yanke hukunci kan cewa Britania ta mayarwa Iran wadannan kudade.
Zareef ya kammala da cewa gwamnatin kasar Britania ta karbi wadannan kudaden ne a tsakanin shekara 1974-76 don sayarwa Iran tankunan yaki samfurin Chieftain guda 1500, amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979, sai takunkuman da turawan tattalin arzikin da turawan suka dorawa JMI suka hanata mika wadannan kudade.