Mai magana da yawun kungiyar, Musa Asake ya shaida wa manema labarai cewa, zargin da ake yi wa Buhari na kokarin musuluntar da Najeriya a fakaice na dada tabbata musammam idan aka yi la’akari da abin da ya faru na kisan jama’a a jihar Benue.
A cewar Asake, Fulani makiyaya na samun kariya a karkashin mulkin Buhari ta yadda suke daukan Najeriya tamkar wani yanki da suka mamaye.
Asake ya ce, a maimakon cafke Fulanin da kuma gurfanar da su, jami’an tsaron Najeriya na ba su kariya duk da aikinsu na ta’addanci.
Sai dai a yayin mayar da martanin, mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam garba Shehu ya ce, abin takaici ne yadda Asake ya gaza bada kwakkwarar hujjar da ke nuna cewa Buhari ya karya dokokin Najeriya.
A cewar Shehu, ya kamata Asake ya tsame kansa daga harkokin siyasa a matsayinsa na jagoran addini