Kotun sojin da ke lardin Iskandariyya na kasar Masar a yau Lahadi ta sanar da cewar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin guda 14, sannan daurin rai da rai a gidan kurkuku kan wasu 'yan kungiyar guda 24, sai kuma wasu 'yan kungiyar ta Inhwan guda 5 da ta daure su na tsawon shekaru 15 a gidan kurkuku.
Kotun ta kara da cewa: Dukkanin mutanen 43 ta same su ne da laifin shiga cikin haramtacciyar kungiya da kuma hannu a kashe jami'in tsaron kasar guda, tada bama-bamai a yankuna daban daban na lardin da kuma kona wasu motoci biyu mallakin ma'aikatar shari'a ta kasar a lokacin tarzomar nuna rashin amincewa da juyin mulki da sojoji suka yi a kasar a watan Yulin shekara ta 2013.