A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Litinin da ke dauke da sanya hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, Jimoh Moshood, rundunar 'yan sandan ta tabbatar wa al'ummomin wadannan jihohin da kada su daga hankulansu don kuwa tuni ta dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.
Mr. Moshood ya kara da cewa tuni Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya din Ibrahim Idris, ya ba wa kwamishinonin 'yan sanda da sauran mataimakan sufeto janar din da suke shiyoyi daban daban na rundunar 'yan sandan a duk fadin Nijeriyan da su kara daukan matakan tsaro musamman a wadannan jihohi da ake magana kansu.
A kwanakin baya ne dai ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniyyan suka bayyana cewar akwai yiyuwar 'yan ta'adda su kai hare-hare a wasu yankuna na Nijeriyan da suka hada da birnin Abuja da kuma wasu jihohi shida na Nijeriyan da suka hada da: Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa da kuma Yobe.