Rahotanni daga kasar sun ce shugaba Mugabe ya isa jami'ar birnin Harare a wurin bikin bada kyautuka na kammala karatu yau Juma'a.
Shugaba Mugabe dai ya ki amunce mika mulki duk da kiraye kirayen ya yi murabus.
Sojojin kasar dai sun ce suna ci gaba da tattaunawa da Mugabe, kuma zasu ci gaba da sanar da al'ummar kasar halin da ake ciki.
Jagoran 'yan adawa na kasar dai ya ce yana da mahimmaci ga kasar idan Mugabe ya yi murabus.