17 Nuwamba 2017 - 14:50
An Raya Daren Wafatin Manzon Allah (s) A Daren Jiya A Duk Fadin Kasar Iran

Mutanen kasar Iran sun raya daren wafatin Manzon Allah (s) da kuma shahadar jikansa Imam Hassan (a) kuma limami na biyu daga cikin iyalan gidansa masu tsarki a duk fadin kasar.

Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da tarurrukan makoki a wurare da dama a duk fadin kasar, musamman a cikin haramomi na Fatima Ma'asuma (a) da ke birnin Qum daga kudancin Tehran, da kuma birnin Mashad inda haramin Imam Rida (a) limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Allah (s) ya ke. 

Manzon Allah (s) ya rasu a ranar 28 ga watan Safar Shekara ta 11 bayan hijira a Madina bayan ya isar da sakon Musulunci ga bil'adama ya kuma kafa daular Musulunci ta farko a Madina wacce ta mamaye mafi yawan kasashen larabawa kafin rasuwarsa. 

Sannan babban jikansa Imam Hassan Almujtaba (a) ya yi shahada ne ta hannun ma'aikatar Mu'awiya dan Abi Sufyan a ranar 28 ga watan Safar Shekara ta 50 bayan hijira yana dan shekara 47 a duniya.

Muna mika ta'aziyyar mu ga al-ummar musulmi kan  wadan nan rashin.