Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Phil Hogan yana fadar haka a wata hira da ta hada shi na kwamishinan a jiya Asabar.
Jami'in na tarayyar Turai ya kara da cewa idan gwamnatin Amurka ta yi watsi da yerjejeniyar shirin makamashin nukliya da ta kulla da Iran, tarayyar Turai ba zata goya mata baya wajen maida takunkuman da aka dorawa Iran a baya ba. Kuma babu wata kasa daga cikin kasashen Turai take da wannan tunanin a halin yanzu.
Phil Hogan ya kara da cewa a wannan shekara tarayyar Turai ta kulla yerjejenita ta bunkasa ayyukan noma da JMI wanda kimansa ya kai Euro Miliyon 10.
A jiya Asabar ne Phil Hogan ya jagoranci wata tawagar tarayyar Turai wacce ta kunshi yan kasuwa 70 zuwa nan birnin Tehran.