Bayanai sun ce Weah ya samu tazara tsakaninsa da babban abokin takarasa Joseph Boakai tsohon mataimakin shugabar kasar.
Alkaluman da hukumar zaben kasar ta NEC ta fitar a jiya sun nuna George Weah a kan gaba da gundumomi 11 cikin 15, a yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'un.
Mataimakin shugabar kasar mai barin gado, Joseph Boakai na kan gaba a gunduma guda inda ya ke a mastayi na biyu a galibin sauren gundumomin kasar.
Kafin dai a ayyana wanda ya lashe zaben don zama shugaban kasa, sai an samu dan takara da ya samu sama da kashi 50% na yawan kuri'un da aka kada, idan kuma ba'a samu wanda ya kai hakan ba, sai a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.