Da yake bayyana hakan kakakin 'yan sanda yankin Nnamdi Omoni, ya dora alhakin mutuwar dan sanda ga 'yan kungiyar IPOD ta masu fafatukar kafa kasar ta Biafra.
Ko baya ga dan sanda da ya rasa ransa da akwai wasu 'yan sanda da dama da suka raunana kana kuma an kone motar 'yan sanda guda.
kakakin 'yan sanda ya ce duk mutanen da aka cafke za'a gurfanar dasu gaban shari'a bayan bincike.
Saboda halin da aka shiga a yankin gwamnan Abia ya ayyana dokar hana fita da dare ta tsawan kwanaki uku tun daga ranar Talata.288