Ana saran wakilai daga kasashen fiye da 90 ne zasu halarciu taron rantsar da shugaba Hassan Ruhani, wanda za'a guadanar a cikin babban zauren majalisar dokokin kasar Iran a gobe Asabar biyar ga watan Augustan shekara ta 2017. Shugaba Ruhani ne ya lashe zaben shugaban kasa karo na 12 tun bayan samun nasarar juyin juya halin musunlin ci a nan Iran. inda ya sami nasara da kuri'u miliyon 23 a zaben da aka gudanar a ranar 19 ga watan mayun wannan shekara.
Shuwagabannin da suka karaso nan Tehran dai sun hada da Ogor Dodon Shugaban kasar Moldova, Richard Bacon shugaban komitin fahintar juna tsakanin majalisun dokokin Iran da Britania. Fonseca Silva's shugaban shugaban komitin hadin guiwa na majalisun dokokin Iran da Potigal, Hassan Sharif shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar Salio, GuanzillesUrbino ministan harkokin wajen kasar São Tomé and Príncipe, Sylvester Bush Matimakin ministan harkokin wajen kasar Hungary, Anwar Mohammad wakilin shugaban kasar Suriname na musamman, Demba Fadiga shugaban majalisar dokokin kasar Guinea, sai kuma Bros GA Darius wakilan kasar Lithuania.
A jiya Alhamis ne aka gudanar da bukin tabbatar da Dr Ruhani a matsayin shugaban kasa a gidan jagoran juyin juya halin musulunci a cikin Husainiyar Imam Khomaini ( r)288