Tashar talabijin ta Al-Hadas ta watsa rahoton cewa: Fira ministan Libiya Fayyaz Assarraj ya bayyana shirinsa na gudanar da zaman tattaunawa da bangarorin siyasar kasar musamman shugabar Majalisar Dokokin Kasar Akilah Salih da babban kwamandan rundunar sojin kasar Khalifah Haftar da nufin samar da hanyar wanzar da gwamnatin hadin kan kasa.
Har ila yau Fayyaz Assarraj ya jaddada aniyarsa ta gudanar da zaman tattaunawa da duk wani bangare kuma daga kowane jiha ta kasar ya fito domin gano bakin zaren warware dambaruwar siyasar da ta wurga Libiya cikin mummunan halin da ta shiga.