Sanarwar da rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA ta fitar ta bayyana cewa an kai wa dakarun hari ne da makamai masu linzame a daidai lokacin da suke kan aikin tallafa wa dakarun Mali domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ana samun karuwar hare-hare akan dakarun na MDD da ma na kasar ta Mali a yankin Kidal da ke kallo a matsayin babbar cibiyar Azibinawa ‘yan tawaye da kuma sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar.