An kai hare haren ne a runfunan ‘yan gudun hijirar da misalin karfe 4:30 na dare, kamar yadda Jami’an da ke kula da sansanin suka tabbatar.
Sai dai babu cikakken bayani akan wadanda suka mutu sakamakon hare hare.
Dubban ‘Yan gudun hijira ne ke rayuwa a sansanin Muna, yawancinsu cikin runfunan kara da suka yi wa kansu matsuguni.
Awwal Janyau da ya ziyarci sansanin a kwanan baya a Maiduguri ya ce ‘Yan gudun hijirar Muna na fama da matsalar abinci da ruwan sha.288