25 Disamba 2016 - 10:38
Al'ummar Tunisia Na Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Dawowar 'Yan Ta'adda Daga Syria

Dubban mutane ne suka gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na kasar Tunisia a jiya Asabar, domin nuna rashin amincewarsu da dawowar 'yan ta'adda 'yan asalin kasar da ke yaki a kasashen Syria da Iraki.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin farar hula da na lauyoyi  a kasar ne suka shirya gudanar da wannan zanga-zanga, inda suke bayyana rashin amincewarsu da kiran da  shugaban kungiyar Al-nahdah Rashid Gannushi ya yi, da ke cewa a yi afuwa ga 'yan ta'adda 'yan asalin kasar Tunisia da ke yaki a Syria da Iraki domin su dawo gida.

Dubban 'yan ta'adda na kasar Tunisia ne dai ke yaki a cikin sahun mayakan kungiyar ISIS a Syria da Iraki da ma kasar Libya,a  ranar Juma'ar da ta gabata ce ministan harkokin cikin gida na kasar Tunisia Hadi Majdub ya bayyana cewa, yanzu haka 'yan ta'adda 800 sun dawo kasar daga Iraki da Syria.

Kasar Tunsia dai ita ce kasa ta biyu bayan kasar Saudiyya wajen yawan 'yan ta'adda da ke yaki a kasashen Syria da Iraki.288