Putin ya ce, amsar da zai bayar kawai ita ce, a ci gaba da yaki da ta’addanci, kuma lalle 'yan ta’adda za su dandana kudarsu.
Shugaban ya ce Rasha za ta tura da masu bincike zuwa birnin Ankara don gudanar da bincike kan kisan, bayan shugaba Recep Tayyip Erdogan ya amince da haka a tattaunawar da suka yi da Putin ta waya.
Shugaba Putin ta ce, dole ne ta gano wadanda ke da hannu a kisan jakadan wanda wani jami'in dan sanda ya bindige a wurin bikin baje kolin hotuna.
Bayan ya harbe shi har lahira, dan sandan ya bayyana cewa, wannan fansa ce akan rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Syria, musamman a birnin Aleppo.