Salihi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Yukiya Amano a yau a birnin Tehran.
Shi ma a nasa bangaren shugaban hukumar kula da makamshin nukiliya ta duniya ya bayyana cewa, wajibi ne a kan dukkanin bangarori da ya hada da Iran da kuma sauran manyan kasashen duniya, da su yi da wannan yarjejeniya kamar yadda aka kulla ta, domin saba wani bangaren yarjejeniyar saba wa kudirin majalisar dinkin duniya ne.
A daya bangaren kuma Yukiya Amano ya gana da shugaba Raunahi, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi shirin Iran na nukiliya, da kuma ayyukan hadin gwiwa da ake yi tsakanin bangarorin biyu.288