4 Disamba 2016 - 12:34
Hukuncin da Kotun Abuja ta yanke da kuma sakin Sheikh Ibraheem Zakzaky..

Babbar kotun Tarayya da ke garin Abuja, ranar Juma'a (02/12/2016) ta yi umurnin a saki Shaikh Zakzaky (H) tare da mai dakin sa, Malama Zeenah Ibrahim; ba tare da wani sharadi ba. Yayin da yake zartar da hukuncin, Alkalin da ke sauraron shari'ar, Gabriel Kolawole; ya nuna cewa ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky da kuma mai.

Babbar kotun Tarayya da ke garin Abuja, ranar Juma'a (02/12/2016) ta yi umurnin a saki Shaikh Zakzaky (H) tare da mai dakin sa, Malama Zeenah Ibrahim; ba tare da wani sharadi ba.

Yayin da yake zartar da hukuncin, Alkalin da ke sauraron shari'ar, Gabriel Kolawole; ya nuna cewa ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky da kuma mai dakinsa da jami'an gwamnati ke yi lallai ya saba wa doka. Mai shari'a Kolawole ya ci gaba da cewa babu wata doka da take wanzuwa a cikin dokokin kasa da ma kasashen waje wacce ta ba da damar a tsare wani mutum ba tare da son ransa ba. Bayan haka kuma, ya yi umurnin a biya Shaikh Zakzaky da matar sa Naira miliyan 25 kowannen su, a matsayin tsare su da aka yi ba bisa ka'ida ba.

Harkar Musulunci a Najeriya ta yi na'am da wannan hukunci wanda ya nuna wa duniya matsayin mu tun bayan harin zalunci da aka kai wa Shugaban mu, 'yan uwanmu da kuma muhallanmu a watan Disambar shekarar da ta gabata, wanda hakan take mana hakkinmu ne na 'yan adamtaka kamar yadda duk wata dokar hankali ta tanadar, wannan hukunci ya tabbatar da haka.

Alkalin ya nuna fahimtar al'amarin baki daya yayin da yake bayani a takaice a kansa, inda yake cewa ya fahimci al'amarin baki daya a matsayin 'kiyayyar' addini, yayin da 'yan Sunnah (mafi yawa) ke zaluntar 'yan Shi'a (kalilan). Lallai haka ne, ya yi gaskiya. An samar da shugabanni a kowane matakin gwamnati domin haddasa kiyayya da bangaranci a addini, da kuma cika burin kasashen ketare. Ta bayyana gwamnatin ta dau wata manufa ce ta musamman inda a farko ta nuna Harkar Musulunci da kuma Shugaban ta a matsayin saniyar ware. Wanda suka yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da mugun nufin su na shafe su baki daya daga doron kasa. Shaidar haka shi ne yadda suka dauki bidiyo a Husainiyya aka nuna a NTA da sauran kafofin yada labarai. Har wala yau, a bayyane yake yadda sojoji da manyan jami'an su suka samu mutane da kuma kungiyoyi da dama suka dauki nauyin su bata Harkar Musulunci a idon duniya, domin su samu hujjar kisan Kiyashin da suka aikata. A kan wannan matashiya ne kuma Alkalin ya fadi cewa, abin da yafi dacewa a nasa hangen shi ne Shaikh Zakzaky da kuma Harkar Musulunci "bai dace a mayar da su saniyar ware ba, lallai suna da 'yancin yin addinin da suka ga dama".

Wannan shari'a ta ta'allaka ne kawai a kan neman 'yanci da hakkin Malam Zakzaky da matarsa. Wannan nasara da aka samu a wannan hukunci babu shakka zai shafi sauran bangarori da yanzu haka ana kan binciken su da kuma wadanda za a fara nan gaba kamar laifin binne mutane a rami guda wanda tuni jami'an gwamnati suka bayyana faruwar sa. Yanzu abin da ya rage shi ne jiran ganin yadda gwamnatin Najeriya za ta amshi wannan hukunci. Ba mu damu da halayyar wannan gwamnati mai ci a yanzu ba, na kin bin dokar kotu ta hanyar ba da uzuri na karya. Za mu ci gaba da fafutukar mu cikin lumana da hakuri har sai adalci ya tabbata baki daya.

Za mu so yin amfani da wannan dama wajen yaba wa duk 'ahalin fafutikar #FreeZakzaky' wanda ya hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, masu rajin kare hakkin dan adam, 'yan jaridu, shugabannin gargajiya, al'umma, siyasa da kuma na addini wadanda suka nuna goyon bayansu a wannan fafutika ta ganin an saki Shaikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba. Kun tsaya mana da addu'a, a zahiri da kuma zuciya har zuwa wannan lokaci. Mun gode sosai, Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi.

A karshe, za mu so mu yi amfani da wannan dama wajen kara matsa lamba a kan wadanda ke tsare da Shaikh Zakzaky da matarsa, cewa dole yanzu su dau matakin barin likitoci, lauyoyi, kowane mutum da su Shaikh ke son gani ba tare da hanawa ba a duk lokacin da suka ga dama. Har wala yau, dole a ba su damar zuwa duk inda suka ga dama, kamar kowa; duk lokacin da suka ga dama saboda su je a duba lafiyar su tunda yanzu kotu ta sake su.

Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya
02-12-2016