29 Oktoba 2016 - 15:39
Wasu 'Yan Kunan Bakin Wake Sun Kashe Mutane A Jihar Borno Da Ke Arewacin Nigeriya

Wasu 'yan kunan bakin wake mata biyu sun tarwatsa kansu a kusa da sansanin 'yan gudun hijiran Bakassi da ke gefe garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.

Kakakin kungiyar bada agajin gaggawa ta Nigeriya "NEMA" Mohammad Kanar ya bayyana cewa: Wasu 'yan kunan bakin wake da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun tarwatsa kansu a cikin daren jiya wayewar garin yau Asabar a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi da ke gefen garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya, inda suka kashe mutane akalla 9 tare da jikkata wasu 24 na daban. 

Wata majiya ta bayyana cewa; 'Yan kunan bakin waken sun nemi kutsa kai cikin sansanin 'yan gudun hijiran ne amma aka hana su, don haka daya ta fara tarwatsa kansa a kofar shiga sansanin, sannan bayan wasu mintoci kasa da 10 na biyu ya tada kanta a gefe guda. 288