An dai tuhimi Ahmad Al Faqi Al Mahdi dai laifin lalata gidan tarihin Tubuctu na Mali dake karkashin kulawar hukumar kare wurare masu tarihi na MDD wato UNESCO.
Ahmad Al Faqi Al Mahdi dai ana tuhumarsa da hannu a laifuka da dama da kuma kasancewarsa kakakin kungiyar mayakan dake ikirarin jihadi a arewacin kasar Mali, kamar yadda daya daga cikin alkalan kotun ta ICC / CPI, Raul Pangalangan ya shaidawa kanfanin dilanacin labarai na Faransa AFP.288