Harin na farko an dai kai shi ne da wata mota a birnin Taji dake arewacin Bagadaza inda mutane a kalla bakwai suka riga gidan gaskia, kana wasu 18 suka raunana a cewar wata majiyar 'yan sanda.
Bayanai sun nuna cewa akwai jami'an tsaro da dama da harin ya rusa.
Harin na biyu kuwa an kai shi ne a daidai lokacin a wata kasuwa dake unguwar Jadida inda mutane 11 suka rasu, wasu kuma 27 suka raunana.
hare-haren kuma a cewar rahotanni sun hadasa barna mai yawa data shafi gidaje da kuma motoci.288