Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu ya ce, an dage ziyarar har nan da bayan azumin watan Ramadan da ake sa ran farawa a cikin wata mai zuwa.
A halin yanzu Buhari na kan fuskantar ayyuka daban daban da lokutansu ke karo da juna, abinda Garba Shehu ya bayyana a matsayin abu mai wahala ga shugaban.
An dai shirya ziyarar ce domin Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a jihar ta Legas amma dai mataimakinsa, Yemi Osinbajo zai wakilce shi a wani yanayi da ba zai dauki hankulan jama’a ba.
Osinbajo zai kaddamar da kananan ayyukan na Legas amma sauran zai bar wa Buhari har zuwa bayan azumin Ramadan.288