Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Sabon Garin Madagali da ke jihar Adamawa, tuni kuma jami'an tsaro suka bazama dan bin sahun 'yan bindigar da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne.
Kamfanin Dillancin labarai na AFP ya rawaito kakakin 'yan sandan jihar Adamawa Usman Abubakar ya tabbatar da sace 'yan matan, haka ma dan majalisa mai wakiltar yankin Adamu Kamale ya shaida aukuwar lamarin.
Maharan sun sace matan ne a lokacin da suka tafi Daji dan yo itace da kuma kamun kifi a wani rafi da ke kusa da kauyen, tare da rakiyar 'yan kato da gora biyu da suke taimakawa sojoji a yakin da su ke yi dan kawo karshen 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.288