26 Afirilu 2015 - 10:08
MILLOLI DA AQEEDU 6 Na Shaikh Hamzah Muhammad Lawal

FA’IDAH TA HUDU Fa’idah ta hudu daga cikin faidojin wadannan darussan shine cewa kila albarkacin darussan mutum ya gane cewa ashe Yan shi’ah suna da hujja akan abinda suke yi, kila ma ya gane cewa abinda suke yi din ma musulunci ne kai kila shine ma musuluncin na hakika,zai iya yiwuwa mutum ya fahimci haka

Kuma wannan yana da dangantaka da fa’ida ta
uku,daga fa’idah na farkon har zuwa na hudun
dukkansu suna bin juna ne.Idan mutum wadannan
shubhohi suka tafi mashi sannan ya fahimci su
aqidun shi’an tana iya yiwuwa ya fahimci cewa ashe
yan shi’ah din
suna da hujja akan abinda suke yi,sannan kuma
abinda suke yi din yana cikin da’iran
musulunci ne, kai shine ma musulunci na gaskiya.To
wannan shi ma ina so in dauki lokaci kila ma ya fi
yalwa akan lokacin da na dauka lokacin bayanin
fa’ida ta uku.
Akwai misalai masu yawan gasken gaske wadanda
mutum zai iya badawa da wasu ababe masu yawan
gaske a fagage masu yawan gasken gaske wadanda
yan shi’a suke aikatawa a fagen hukunce hukunce
da fagen i’itiqadi da fagen siyasa da fagen
zamantakewa da
kuma fagage daban daban wadanda wadannan
ababen baki ne a idanun mutane sosan gasken gaske
amma kuma a asalin addini suke,abinda ya faru
kawai shine cewa su Yan shi’a sune suka dage suka
kadaita da aikata wannan bangaren na
addinin.Wannan da’awa ce wadda nayi.
MISALAN ABUBUWAN DA YAN SHI’AH SUKA DAGE
AKANSU KO KUMA SUKA KADAITA DASU AMMA
KUMA TABBATATTU NE A ADDININ MUSULUNCI
Insha’Allah zamu yi kokari mu kafa dalili,idan zan iya
bada misali kadan daga littafai a janibin Ahkam a
cikin hukunce hukunce,akwai abinda ake ce ma:-
***AT-TAKFIR***
At-takfir wato At-takattum wato Rufewa,daga nan ne
kalmar Kufur tazo wato rufe abu wannan ne yasa
Allah yake ce ma manomi KAFIR wato kenan ZAARII
ko kuma kace FALLAH.Yana ce mashi KAFIR ne
saboda yana rube hatsi a kasa,ma’anar KUFUR ko
TAKFIR anan wurin muna nufin da ma’anar rufe
hannu daya akan daya a lokacin kira’a a sallah
wanda yin wannan wani lokaci akance mashi AL-
QABDU.
Idan ya zama cewa abinda aka shar’anta a
mazhaban mutum shine damkar hannun hagu da
hanun dama wani lokaci kuma akance mashi AL-
WAD’U,idan abinda aka bukata daga mai sallah shine
dora hannun dama akan hagu.To Yan shi’ah basa yin
wannan wato basa yin TAKFIR.
ME YASA YAN SHI’AH BASA YIN AT-TAKFIR?
Duk da yake ba wai muna so mu shiga cikin fiqhun
bane,muna so muce ne shi wannan abin baya daga
cikin addini,mu Yan shi’ah muna da i’itiqadin cewa
yana bata sallah kuma baya da asali.Akwai ruwayoyi
da suka zo a cikin Sahihul bukari da Sahihu
musulim,kamar irin ruwayoyin Sahal bn Sahal As-
sa’idiy a cikin Bukari da kuma wata ruwayan a cikin
Musulim wadda Yan shi’ah suna iya wajjahasu kuma
suna iya taujihin su ko kuma suna fuskantar dasu su
auwalasu su yi masu tawili.Wani lokaci suna iya bata
su ma gaba daya duk da yake sun afku a cikin Buhari
da Musulim saboda irin wadannan wata rana zai
zama wajibi akan mu mu yi bahsi akan Sahihul
Bukari da Sahihu Muslim amma yanzu duk wannan
muna shirya kwakwalen mutane ne saboda abinda
muke so mu je zuwa gare shi din ne a tsakiyan
bahasin mu.
Ruwayar Sahal wadda ta afku a cikin Sahihu Muslim
cewa:-
“HADDASANA ABDULLAH BN MUSLIMAH,AN MALIK
AN ABIY HAAZIM AN SAHL BN SA’ADIN,QALA
KANAN NASU YU’UMARUNA AN YADA’AL YUMNA
ALA DHIRAA’IHIL YUSRA FIS SALATI,QALA ABU
HAAZIM LA A’ALAMUHU ILLA YANMIY ZALIKA ILAN
NABIY SALLALLAH ALAIHI WA SALLAM”.Ma’ana:
-“…..Mutane sun kasance ana umurtan su a zamanin
Annabi{saaw}akan su dora hanun su na dama akan
zira’in su na hagu.”
Wanda duk ya san larabci ya san cewa wannan
jumlar an gina ta ne akan Majhul wato ba a san
wanene mai umurnin{AMIR}ba, wanene mai umurnin?
Annabi{saaw}ne ko wanene?Wannan shine farkon
fiqhun ruwayan ba kuma ina so in shiga cikin shi ne
gabaki daya ba.Sannan ruwayar muslim ta zo ne
akan cewa Manzon Allah{SAAW}ya zo sallah sai ya
tattaro tufafin shi,wato yana nuna kamar ya tattaro
abayan shine ya rike, wanda in wannan ya afku
sunan shi Sunnah Fi’iliyyah,wanda daidai.ABNA