15 Afirilu 2015 - 07:40
Hatsarin jirgin ruwa ya halaka 'yan kasar Libiya 400

'Yan kasar Libiya kimanin dari hudu ne hatsarin jirgin ruwa ya halaka yayin da su ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Italiya.

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda wasu da suka tsira da ransu suka tabbatar.

Wani jami'in tsaron gabar kogin kasar Itlaliya, ya ce sun ceto mutane 144 tare ma da gano wasu gawawwaki 9, a hatsarin da aka ce ya faru ne sa'o'i 24 da jirgin ya bar kasar Libiya kan hanyar zuwa Italiyan.

Kungiyar shige da fice ta duniya tare da kungiyar samar da agaji ga kananan yara ta Save the Children, sun ce kawo i yanzu dai akalla akwai mutane 150 suka tsira, cikinsu kuwa harda yara kanana 'yan maza da dama.

Wani mai magana da yawun kungiyar shige da ficen na duniya, Flavio Di, ya shaidawa kamfanin labaran Faransa AFP cewa, jirgin na shake ne da mutanen da basu kasa 550 ba, a lokacin da ya nitsen

An dai danganta wannan lamarin da rikicin kasar Libiya da a yanzu ke tilasatwa mutane tururuwar tserewa zuwa wasu kasashe.ABNA