MA’ANAR AL-WAD’U DA ISTI’IMAL Akwai abinda ake ce ma Al-wada’u wanda shi abinda yake takaffuli shine ya ajiye kalma domin wata ma’ana,kamar kalman {Ma’uun;}wato {mim,alif,hamza}ma’ana kalmar Ruwa kamar yadda bahaushe yake kiran shi.In bahaushe yace ruwa abinda yake nufi shine ruwa wannan wanda yake kwarara a kasa busassa(Qashar) wanda yake kashe kishi,to in kaji bahaushe yace ruwa to a binda yake nufi kenan,wannan shine wazifar Al-wad’u. Amma Isti’imal din wannan kalma kuwa shi yafi yalwa daga wad’u shi yasa malaman Usul suna da qa’idan da suke ce ma ta:-“AL-ISTI’IMALU A’AMMU MINAL HAQIQATI WAL-MAJAZ”ma’ana yin amfani da isti’imal yafi yalwa daga hakika da majazi,saboda wani lokaci ana yin amfani da kalma haqiqi,ma’anar haqiqi shine ayi amfani da kalma a abinda aka a je ta domin shi,wani lokaci ana isti’imal din kalma a Majaziy har ta fita daga cikin abin da aka ajiye ta domin shi tun daga asali,misali zaka iya amfani da kalman {zaki} ka nufi jarimi,shi ya sa duk lokacin da a kai amfani da kalma wadda tafita daga qa’ida ana kafa mata qarina ne,kamar yanzu in kace “Na ga zaki na tuka mota”to yana tuka mota din itace karinan da ka kafa wannan shi yake nufin ba wancan zakin da yake cikin daji bane kake nufi,wannan zakin a cikin gari yake kuma kafafuwan shi biyu ne,mutum kake nufi kawai a taqaice. Saboda haka akwai mishkila tare da wadanda suke daukan nassosi su yi amfani dasu,ko ma’abota shubha da suke daukan nassosi suna mu’amala dasu a kowanne irin lokaci,wannan akwai mishkila a cikinsa sosai kuma ba zamu shiga wanann ba yanzu ba,amma yanzu maudu’in mu shine nassin aqidun shi’ah wanda wasu ke dauka suyi amfani dasu ba tare da muraja’an yan shi’an ba. Na farko basa iya banbancewa tsakanin Al- wada’u da Al-isti’imal,sannan na biyu zai iya yiwuwa su suna magana ne akan asasin Ad-dalil At-tasauwuri ko Ad-dilalah At-tasauwuriyah ta wannan kalma din a cikin lugah amma kila su ma’abota nassosin suna magana ne akan asasi ko mustawa ta Ad-dilalah At-tasdiqiyah As-saniyah,zan yi bayanin abinda nake nufi.Kuma matukar rutubobin nan sun banbanta ba za a fahinci abinda ake nufi ba saboda wannan yana magana akan Ad-dilalah At- tasauwuriya Al-wad’iyyah Al-lugawiyyah shi kuma wancan yana magana ne akan asasin Ad-dilala At-tasdiqiyyah Al-ula ko As-saniyah?As-s aniyyah,zasu fahimci junan su?In ba a mai da hankali ba sai wanda yake magana akan asasin Ad-dilalah At-tasauwuriyyah sai ya zama kaman mutumin da aka ce mashi { WATARA KUKA QA’IMAN} sai ya fassara da cewa sai naga itacen kuka a tsaye,ko kuma {LI TUNZIRA QAUMAN LUDDAN} sai yace da suka tunzura sai suka karya ludduna.Lafazi nada abinda ake ce ma Ad-dilalah At-tasauwuriyyah. MA’ANAR AD-DILALAH AT-TASAUWURIYYAH Ad-dilala At-tasauwuriya itace wannan ma’anar da mutum ke surantowa a kwakwalwar shi lokacin da aka ambaci lafazin,kamar misali in ce ruwa,to wannan suran daka suranta a kwakawalwarka ko ka sawwala lokacin da ka ji ance ruwa ita ake ce ma Ad-dilalah At- tasauwuriyyah wato dilala wadda ka suranta ka zuciyarka wanda ke takaffufinta shine Wad’u kuma baida banbanci ko daga ina kaji kalman ruwa kasan me ake nufi, ko daga kaset ko daga ina ka ji kalmar ruwa,me zaka sauwala?ruwa,wannan ma’anar shine wazifar Ad-dilala At-tasauwuriyyah ko kuma kace wazifar wad’u kawai itace domin ta haifar maka da wannan kalma din a cikin lugah amma lokacin da kaji kalman ruwa daga mutum mai hankali a farke ba ya bacci ya san abinda yake nufi {multafit} za kace akwai Al-qasdu a cikin wannan mutumin wato akwai manufa,sabanin da a ce ka jita ne daga kaset ko mai bacci ko ila kirihi in dai akwai manufa to shi kenan,manufar kuma itace {Al-iqdar} yana so ya haifar maka da ma’nar ita kalma din ne,saboda haka in yace ruwa ina nufin wannan abinda ka fahimta a dilala ta farko wato Ad-dilala At-tasauwuriya. MA’ANAR AD-DILALAH AT-TASDIQIYAH AS- SANIYYAH Abinda muke nufi da Ad-dilalah At-tasdiqiyyah As-saniyyah itace wannan wadda itama akwai nufi a cikin ta amma ta wuce qasdil ikdar kawai,ya wuce ace qasdin ya haifar maka da ma’ana kawai,yanzu qasdin {Al-ikbar wal-hikaya} yana so ya baka labarin cewa ruwan fa nake nufi yana so ya hikaito maka wancan ma’anar da ka sani a mustawan Al-wad’u da kuma At-tasauwur,wato akwai jiddiya da gaske yake yi saboda haka lokacin da kaji kalmar ruwa daga mutum kana bukatan kai intiqali daga dilala ta farko zuwa ta uku,wato “ jiddiya” da gaske wannan ruwan yake nufi ko ba wannan ruwan yake nufi ba?ka gane ma’anar bahasin a taqaice?cewa da gaske ruwan yake nufi ko ba shi yake nufi ba?to wani lokaci zai zama da gaske yake yi sai ya zama Isti’imal din ya zama Haqiqiyyah,In ko ya zama a’a wani abu daban nake nufi ba wannan ruwan ba to sai ya zama isti’imal din mu ya zama Isti’imal ne Majaziy. Saboda haka in kaji kalmar Taqiyyah,Ar-raj ’ah,Bada,Mus’haf da sauransu da sauransu, baka da hakkin ka yi amfani da ma’anonin lugah ka yi hukunci akan mutane da wadannan manoni na lugah,in kai haka sai ya zama kila ba shubhohi kake dashi ba a’a wahamomi(Auham) kake dasu amma lallai kai masani ne a Al-ilmul husuli domin dabbaquwan suran abu a kwakwalwa wanda tunda ilimine husulliy wanda ake samu ta hanyar hawas zai iya zama musiba,da gaske abinda kai ka ga ni ba shi ne kake tsammani ba saboda haka zaka iya ka kuskure sabanin Al-ilmul huduri wanda shi ba a kuskure sabo da shi huduru nasish shai’i ladal Aalim ne shi ba a kuskure a cikin shi.Akwai karkasuwan Al-ilm Al-huduri wanda kuma ba shine bahasin mu ba anan wurin.Ala kulli hal Allah yana cewa:-‘Wala Taqfu ma laisa laka bihi ilmun,Innas sam’a wal-basra wal-fu’ada kullu ula’ika kana anhu Mas’ula”ma’ana “kada ka bibiyi abinda baka da ilimin shi,saboda jinka da ganin ka,da zuciyan ka,kowanne daga wadancan dinka ya kasance abin tambayo ne” Sannan Al-imam Sadiq{as} ya gaya mana a cikin hikimomi cewa:-“Min Aklaqil Jahil,Al-ijabatu gabla an yasm’a,wal mu’aradatu qabla an yafham,wal hukmu bima la ya’alam”ma’ana “Yana daga cikin dabi’un jahili, akwai bada amsa kafin yaji,zai baka amsa alhali baiji karshen tambayan ba,za kai mashi tambaya akan menene wannan? Sai ya baka amsa akan wanene wanan?ko al-aksu.Jahil haka yake,da kuma gardama da bijirewa kafin ya fahimta,shi jahil bai fahimci maudu’in ba amma sai ya fara mu’arada bi shikkil amfusi yana so sai ya rusa wannan abin da bai san shi bBa din,kamar yadda Imam Ali {as] yake cewa su mutane suna gaba da abin da basu sani ba(wato An-nasu A’ada’u ma Jahilu),Saboda haka jahili zai zama yana mu’arada da abinda bai fahimta ba,da kuma hukunci da abin da bai sani ba wato hukuncin da yake fadin ba dai dai bane amma yana yi saboda haka wannan yana da muhimmancin gasken gaske.Ba wadannan bane dabi’un shi akwai wasu shi yasa Imam Sadiq yace Min Aklaqin Jahil…saboda haka akwai wasu banda wadannan guda ukun. Wannan shubuhohin da da’iran Lugah kenan banda haka akwai shubhohi a da’irori dabam dabam.kamar Isara da karya da kaqe,za su iya cewa Yan shi’ah gabaki dayansu suna alfari Imam Husain ne saboda mahaifiyarsa Bafarisa ce wato Imam Husain Bafarise ne shi ma wai duk A’immah suka zama jikokin Imam Husain sabanin Hasan(as).kai kace Yan shi’a suna fada da Imam Hasan,basu san matsayin Imam Hasan a wurin su Yan shi’a din ba.ABNA
5 Afirilu 2015 - 07:18
News ID: 681297

Na Shaikh Hamzah Muhammad Lawal