Kamfanin Dillancin Labarai na IRINN- jami'an leken asiri na kasar Turkiya na fargabar yiyuwar kaima wuraren kasashen Turai da suke kasar hari, idan akai la'akari da yawaitar yan kasar a cikin kungiyar nan ta takfiri wato Da'ish ruhotanni na nuni sama da yan kasar 3000 ne suke da alaka da wannan kungiya.
Kuma wannan wata barazanace ga hukumar tsaro ta kasar, jami'an dai na cikin zaman dar-dar da shirin ko ta kwana domin kare dun wani hare da yan ta'addan zasu iya kama ofisoshin jakkadanci kasashe Turai da kuma ofishin Nato.
In ba a manta ba a makon da ya gabata ne wasu yan bindiga suka kai hari a paris babban birnin Faransa.Abna