Sai dai har yanzu shugaban Nigeria Goodluck Jonathan bai ce uffan ba game da hare-haren duk da yake daruruwan mutane sun mutu.
Wata sanarwa da ofishinsa ta fitar, Mr Ban ya ce ya yi matukar kaduwar da jin labarin hare-haren, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Ya bayyana hare-haren a matsayin na ta'addanci.
Mr Ban ya ce a shirye yake ya hada gwiwa da hukumonin Nigeria domin taimakawa mutanen da lamarin ya shafa.ABNA