Daga taskar labarai ta ahlulbait{a.s} – Ayaullahi subhani wanda shine ya rufe taron da akayi kwana biyu na gudanarwa akan hadarin akidar masu kafirta musulmi a mahangar maluma, kuma wanda shine shugaban bangaren ilimi na wannan zaman. Da farko yayi godiya ga mahalarta taro ya kuma kara da cewa; masana da maluma da yawa sun amsa kiranmu kuma sun rubuta makaloli masu amfani wanda in aka fassara su zuwa harsuna daban daban tabbas zasu amfanar da duniyar musulmi, kuma fatawowin da maluma zasu daba za suyi amfan ya kuma roki Allah da ya da ladar akan mahalarta taron.
Ayatullahi subhani ya kara da cewa; acikin wasu bangare na makalolin da aka rubuta akawo shawarwari akan yadda za a makance wannan mumunar akida. Da haka zamu iya fahimta cewa dukkan mahalarta taron suna Allah wadai da akidar kafirta musulmi kuma kowa ya yada da cewa cewa Allah bai yada da wannan akidar ba dukkan maluman addini sun hadu akan cewa shari’ace kawai zata fitar da mutun daga da’irar musulunci.
Ayatullahi yace; ina Allah wadai da wannan akidar kuma sun sabama akidar musulmi ya kara da cewa kafirta musulmi baba’ine ciwone wanda wa tsiro da tsakanin musulmi, minene mafita?
Subhani yace; taro da kuma rubuce-rubuce ba zasu kawar da wannan akidar ba, saboda haka ya zama dole musamar da hanyar kawar da wannan akida daga tushe.
Sanar da mutane hadarin wannan akida ta hanyar kafafen labarai, da masallata sune hanya ta farko ta yaki da akidar, yace dole mu kawar da mumunan halaye acikin al’umma. Ayau masu kafirta musulmi suna kasha wanda ke sallah yana kuma zuwa hajji a matsayin kafiri amma sun sa ido suna kallan sahayoniyawa suna cin Karen sub a babaka.
Yada al’adun musulunci na gaskiya shine hanya ta biyu, domin al’adar musulnci shine duk musulmi yan uwan juna ne kuma musulunci yana kiran kowa da kowa zuwa ga zaman lafiya. Saboda haka al’adar musulunci ta haramta jinin musulmi .amma wannan akidar ta masu kafirta musulmi sun bata sunan musulunci sun maida fuskarsa addini shan jinni.
Ayatullah ya kara da cewa; taruruka na ilimi suna daya daga hanyoyin kawar da wannan akidar don haka ya kamata acigaba da gudanar dasu. Saboda haka ire-iren wannan taron wana da amfani domin zai hada kan maluma wuri daya wanda yanzu haka ke faruwa kuma da fatan mahalarta taron in sun koma kasashen su zasu isar da sakon da suka samu daga wannan taron, kuma dole a yada hadarin wannan akidar acikin kafafen yada labarai na duniya domin matasan mu su san hadarin wannan akida mummuna.
Hanya ta hudu itace komawa ga littafai na asali domin musulmi muna da bam-bamci acikin akida da fikihu don haka in kana son kasan wata mazahaba dolene ka koma acikin littafin ta na asali wanda masanan wannan mazahaba suka rubuta, amma abun bakin ciki shine maluma basa aikata hakan kuma wannan kuskure ne.
Kwaskwarima ka littatafan karantarwa a makarantu wanda sune suke sa matasa fadawa cikin wannan akida abun bakin ciki wasu kasashen acikin littafan koyarwarsu suna yada maganganun fitina . kamar haka { shirkar makabata bata kai shirkar nayizu ba ko kuma tawasali da annabawa shirkace} amma kuma acikin irin wannan akasashe ake bada izinin bugawa, ta haka ne matasan mu ke badawa cikin ta’addanci.
Ayatullahi subhani; tushen kafirta musulmi ya samo asaline daga kuskuren fahimta ta imani, tauhidi,kafirci, shirka, bidi’a don haka ya kamata ayi zaman na musamman akan wadannan abubuwan biyar, saboda masu kafirta musulmi suna amfani da ayoyin da suka sauka kan mushirikai akan musulmi.
Daga karshe yace kasashen turawa suna nuna fuska biyu wurin fada da ta’addanci wani wuri su yabi yan ta’adda awata kasar su soki ta’addanci. Ya kuma roki Allah da ya maida kowa kasar su lafiya. ABNA