Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Jagoran ya tunatar da al’umma muhimmancin haɗin kai da komawa ga sahihin koyarwar addinin da Manzon Rahma (S) ya zo da shi. Ya ce: “Manzon nan ya zo da addini kammalalle, cikakke, kuma ya ɗora al’umma a kai. Abin da ya hau kanmu shi ne mu bi.”
Ya ƙara da cewa, maƙiya na ƙoƙarin aibata shaksiyar Manzon Rahma (S) saboda sun fahimci Musulmi sun riƙe sa a matsayin ramzi a raruwarsu.
Haka kuma, ya ja hankalin al’umma kan rigingimun da ake haddasawa tsakanin Musulmi, inda ya bayyana cewa irin waɗannan rigingimu, da sunan addini ne ko ƙabilanci, ba za su amfanar da al’ummar Musulmi ba, sai dai su maƙiyan da ke haddasa su domin amfanin ƙashin kansu.
Yace, maƙiyan ne ke haddasa rigingimu da matsalar tsaro domin ɗauke hankalin mutane, yayin da suke satar dukiyoyinmu tare da ƙara jefa mutane cikin talauci da rarrabuwa.
Jagora ya bayyana cewa, fahimtar wannan salon maƙiyan, haɗin kan al’umma da koma wa sahihin koyarwar Manzon Rahma (S) ne zai kawo mafitar matsalolin da ake fuskanta.
Taron wanda Dandalin Resource Forum suka saba shiryawa a duk shekara, na yau, ya samu halartar mahalarta daga sassa daban-daban na al’ummar Musulmi, ciki har da limamai, malamai, ma’aikata da sauran al'umma. An fara shi ne da misalin karfe 10:00 na safe, zuwa karfe 2:00 na rana.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
01/RabiuThani/1448
13/09/2026
Ra'ayinka