Sanarwar rufe masalacin na kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis ya fusata mazauna birnin na Qudus,kamar kuma yadda gwamnatin Palasxinawa ta bayyana shi a matsayin shelanta yaqi akan al’ummar Palasxinu da kuma musulmi. Kamfanin Dillancin Labarun (a.f.p) ya nakalto cewa; An sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Qudus bayan da a wunin jiya aka yi batakashi tsakanin matasa da jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila. Sai dai duk da bude masallacin kudus, yan sahayoniya sun gindaya sharadin cewa wadanda shekarunsu ba su kai 50 ba ba za su shiga masallacin ba domin yin salla. Keta hurumin masalalicn Kudus dai ya zama wani abu da yahudawa ‘yan share wuri zauna su ke yi a kowace rana ta Allah ta hanyar kutsawa cikinsa. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rufe masallacin na Kudus, tun wanda ya faru a shekarar 1976. ABNA
31 Oktoba 2014 - 19:48
News ID: 648287

An sake buxe masallacin Kudus bayan rufe shi da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis.