11 Oktoba 2014 - 15:22
Sojojin Niger Sun Fatattaki Wata Ayarin Yan Ta'adda A Rewacin Kasar Dauke Da Dimbin Makamai Zuwa Mali

Sojojin kasar Niger sun bada sanarwan tarwatsa wata ayarin yan ta’adda wadanda suke dauke da makamai daga kasar Libya zuwa kasar Mali.

Shafin yanar gizo na African Times ne ya bada wannan labarin sannan ya kara da cewa ayarin yan ta’addan yan kungiyar Al-qa’da ta fito ne daga kudancin kasar Libya inda take dauke da makamai masu yawa don kaiwa yan ta’adda a arewacin kasar Mali.

Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Faransa wadanda suke da sansanin jiragen yaki a bakin take sun taimaka wajen tarwatsa tawagar yan ta’addar.

A cikin watan satumban da ya gabata ma sojojin na Niger sun fattaki wasu yan ta’addar yan kungiyar Al-qa’ida wanda ya kai gaba kama wani na kusa da Mokhtar Belmokhtar shugaban yan kungiyar a kasar Algeria. ABNA