2 Oktoba 2014 - 09:58

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta kara wa’adin ayyukan da take gudanarwa a kasar Liberiya saboda ci gaba da yaduwar cutar nan ta Ebola da kuma wajibcin kara kaimi wajen fada da ita.

Kamfanin dillancin labaran Xianhua na kasar China ya bayyana cewar a daren jiya Laraba ne kwamitin tsaron MDDn ya sanar da kara wa’adin ayyukan MDDn har zuwa ranar 15 ga watan Satumban 2015.

 

Har ila yau yayin da yake magana kan hakan, Karin Landgren, wakiliyar babban sakataren MDD, Ban Ki Moon, sakamakon ci gaba da yaduwar cutar Ebola a kasar Liberiyan ne ya sanya kwamitin tsaron MDDn dakatar da duk wani shiri na dawo da jami’an majalisar daga kasar Liberiyan.

 

Tun a shekara ta 2003 ne MDDn ta tura dakarunta kasar Liberiya da nufin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar sakamakon rikici da yakin basasa da ke gudana a lokacin. ABNA