26 Satumba 2014 - 21:25
Sheikh Siddiqi: Shugaban Iran Ya Isar Da Sakon Mutanen Kasar Ga Duniya

Limamin da ya jogoranci sallar jumma’a a nan Tehran Sheikh Kazim Siddiqi ya yaba da jawabin da shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Ruhani a gabatar a babban zauren Majalisar dinkin duniya a jiya Alhamis, inda ya isar da sakon mutanen kasar Iran da kuma wadanda ake zalunta a duniya ga kasashe masu girman kai.

A wani bangare na khudubarsa Sheikh Saddiqi ya yi ishara ga yakin kare kai na shekaru 8 wanda JMI ta shiga a farko farkon jiyun juya halin musulunci wanda ya zama alkhairi ga mutanen kasar ya kuma daukakasu ya daukaka addinin musulunci a duniya.

Limamin ya kara da cewa jinin shahidan JMI da kuma wadanda suka sami nakasa a wannan yakin sun zama matakala wadanda mutanen kasar da kuma kasar suka hau don samun daukaka.

A karshen khudubarsa ta farko limamin ya yaba da yadda mutanen kasar Iran kama daga Jami’an gwamnati da kuma sauran mutane suka nuna damuwarsu kan aikin tiyata da aka yiwa jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khami’aee a makon da ya gabata. ABNA