23 Satumba 2014 - 08:52
Mutane 11 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Makamai A Barikin Soja Na Albaida

Kimanin Mutane 11 suka rasa rayukansu sanadiyar wani hatsari a barikin soja dake birnin Baida na Kasar Libiya. A wani rahoton da ta fitar, Majiyar tsaron kasar Libiya ta tabbatar da mutuwar Mutane 11 sanadiyar fashewar wani abu a runbun tsumi barikin Soja na Albaida dake gabacin kasar ta Libiya.

Rahoton ya ce mai yiyuwa tsananin zafi ne ya janyo fashewar wannan makamai.

 

Kasar Libiya dai na fama da rikici tun bayan faduwar Gwamnatin kanal Mu'amar Gaddafi a shekara ta 2011, inda a baya bayan nan ake gobza fada tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar, a bangare guda kuma tsakanin 'yan bindigar da sojoji masu biyayya da tsohon janar mai ritaya khalifa Haftar.   ABNA